1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenyata ya zargi Kotu da yin juyin mulki

Abdul-raheem Hassan
September 21, 2017

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyata ya soki matakin kotun Kolin kasar da yin juyn mulki, inda ya ce hukuncin da ya haramta nasarar zabensa a matsayin sabon shugaban kasa ya yi sabani da ra'ayin al'ummar kasar kenya.

https://p.dw.com/p/2kTWR
Kenia nach der Annulierung der Präsidentenwahl | Uhuru Kenyatta
Shugaban kasar Kenya, Uhuru KenyataHoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

Kenyata ya yi wadannan kalamai ne a yayin da ya ke tsokaci a gidan talabijin na kasar, bayan da kotu ta sanar da matsayanta kan hujjojin soke zaben. Shugaban ya ce 'yann adawa sun yi amfani da kotun wajen yin juyin mulki.

Hukuncin kotun na ranar 1 ga watan Satumba shekara ta 2017, shi ke zama hukuncin kotu na farako da ya yi tasiri wajen rusa zaben shugaban kasa a nahiyar Afirka. A yanzu dai a ranar 17 ga Oktoban da ke tafe ne kotun kolin kasar ta Kenya ta bada umarnin sake shirya sabon zaben shugaban kasar.