1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya ta nemi hana cinikin hauren giwa

Suleiman BabayoApril 29, 2016

Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ya nemi kawo karshen cinikin hauren giwa saboda kare su daga bacewa daga doron kasa na nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/1IfM2
Deutschland Uhuru Kenyatta in Berlin
Hoto: picture-alliance/NurPhoto/E. Contini

Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya ya bukaci ganin an haramta cinikin hauren giwa, domin kawo karshen cinikin bayan fage da kare giwaye daga bacewa daga doron kasa. Shugaban ya fadi haka wajen taron da kasarsa ta dauki nauyi na kasashen Afirka wadanda suka tashi tsaye domin kawo karshen kashe giwaye da barayi ke yi.

Wani bincike ya nuna kasashen Afirka suna da giwaye tsakanin 450,000 zuwa 500,000, amma kowace shekara kimanin 30,000 barayi ke kashewa domin saye da hauren ta barauniyar hanya, galibi a kasashen yankin Asiya, a kan makudan kudade. Tuni kasashe da dama na Afirka da hadi gwiwa na 'yan kasuwa masu kansu suka fara aikin tare domin kare damun daji.