Kenya ta gaza daukar wasannin ′yan Afirka | Labarai | DW | 24.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kenya ta gaza daukar wasannin 'yan Afirka

An yanke wannan hukunci ne a wani zama da manyan jami'ai na hukumar CAF suka yi a birnin Accra na Ghana a ranar Asabar.

Kasar Kenya ta rasa dama ta daukar nauyin wasannin zakarun da ke taka kwallo a nahiyar Afirka ta CHAN a shekarar 2018 mai zuwa. Hukumar da ke tsara wasannin na Afirka CAF ta ce kasar ta Kenya ta yi nauyin jiki a kokari na shirye-shiryen karbar bakuncin wasannin na nahiyar da zakaru daga kasashe ke halarta.

An yanke wannan hukunci ne a wani zama da manyan jami'ai na hukumar suka yi a birnin Accra na Ghana a ranar Asabar kana a wannan rana ta Lahadi a ka bude dama ga sauran kasashen da ke da sha'awar daukar nauyin wasannin na CAF da su gwada ta su sa'ar su nema, kuma a cewar hukumar  kasashen da ke da muradi na da nan zuwa Lahadi mai zuwa su aika da bukatarsu, yayin da kasar da ta yi nasara za a bayyanata nan da makonni biyu.

An dai tsara buga wasannin ne tsakanin 12 ga watan Janairu zuwa hudu ga watan Fabirairu mai zuwa. Kamar Kenya ita Kamaru za a yi nazari kan shirye-shiryenta na karbar bakuncin wasannin a shekarar 2019.