1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya ta faɗa rikicin siyasa

Ibrahim SaniDecember 31, 2007
https://p.dw.com/p/CiJC

´Yan sanda a Kenya, sunyi amfani da barkonon tsohuwa don tarwatsa gungun Matasa, dake zanga-zangar adawa da Gwamnati. A yanzu haka dai anyi asarar rayuka bakwai, sakamakon arangama a tsakanin ɓangarorin biyu. Matasan a cewar rahotanni na ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, daya bawa Mr Kibaki nasara. Jam´iyyun adawa ƙarƙashin Raila Odinga, sun zargi Gwamnati da yin maguɗi a cikin wannan zaɓe. Tuni dai Mr Mwai Kibaki ya karɓi rantsuwa, a matsayin tazarce na tsawon shekaru biyar a karo na biyu a jere. A lokacin yaƙin neman zaɓe, Mr Kibaki ya yi alƙawarin mayar da ilimin firamare da sakandare kyauta, a hannu ɗaya kuma da inganta tattalin arziƙin ƙasar.