Kenya ta cafke wani shugaban kotunan musulunci | Labarai | DW | 15.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kenya ta cafke wani shugaban kotunan musulunci

Jamian tsaro a kasar kenya sunce sun tsare wani shugaban kotunan musulunci na Somalia a yankin Garissa dake kusa da bakin iyaka kasar.

A wani labarin kuma wasu yan bindiga sun bude wuta kann tawagar dakarun Habasha dana Somalia a cikin birnin Mogadishu suna masu lalata motocin da suke ciki sai dai har ya zuwa yanzu babu rahoton yawan wadanda suka jikkata cikin wannan bata kashi ba aka kwashe kusam mituna 30 a nayi.

Sojojin gwamnati dana Habasha dai sun kaddamar da bincike gida gida don zakulo wadanda suka kai wannan hari.

A yau ne kuma shugaban Somalia Abdallah Yusuf ya nada sabon magajin garin Mogadishu,mataki da jamian diplomasiya suke gannin mai muhimanci ne na tabbatar da ikon gwamnatin ta Somalia.

Kanfanin dillanci labaru na AP kuma ya sanarda cewa,wani babban jamiin gwamnatin wucin gadin ta Somalia ya bada umurnin a rufe wasu gidajen radiyo uku na Somalia da kuma ofishin gidan TV na aljazeera ba tare da bada dalilan yin hakan ba.