1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya: Sauya hanyoyin tafiyar da tattalin arziki

Dominik v. Eisenhardt-Rothe/ SBApril 13, 2016

Kenya na da kamfanoni da yawa da ke zama kara zube, amma suna da kwararrun ma'aikata da kuma sanin da ya dace a yi aiki da shi amma ba a yi.

https://p.dw.com/p/1IUVb
Africa on the Move Kenia - Videostill
Hoto: DW

Wane sashe na kamfanonin da ke taka rawa a tattalin arzikin kasar Kenya ya kasance na kara zube, akwai wadanda suke da kwarewa da kuma sanin da ya dace a yi aiki da shi amma ba a yi. Wannan tunani ya fado wa Catherine Gichunge wata matashiya lokacin da take neman wanda zai yi mata aikin gyaran gida. Ta yi amfani da wannan damar wajen sauya hanyoyin tafiyar da tattalin arziki a Kenya.

A Kenya dai ma'aikatan gyaran ruwa suke gyara hanyoyin ruwan kichin idan aka samu toshewa. Ba wai babu wadanda suka iya gyara ba ne, sai dai babbar tambayar yadda za ka samu masu gyaran a hukumance. Wannan matsala ce da Catherine Gichunge ta ci karo da ita kuma ta kawo wata mafita:

"Kowane lokaci na tambaya makwabta sai an nemi taimakon yadda za a samu mai gyaran hanyoyin ruwa na gida, ko mai gyaran wuta, kuma na lura wasu suna aikin maras inganci. Na ci gaba da rayuwa haka har zuwa lokacin da na ce mai zai sa ba zan fita ba. Akwai mutanen da suke da kwarewa, ba su da Intanet, idan na kai musu hanyar sadarwa ta Intanet za ta taimaka musu wajen gudanar da aikinsu."

Intanat ga masu sana'ar hannu

Daga nan sai Catherine Gichunge ta yanke shawarar kirkiro wata hanyar ta Intanet da za ta taimaka a samu masu aikin hannu wadanda suka kware wajen amfani da Intanet da kuma wayoyin hannu.

"Na duba akwai wata tazara. Akwai mutanen da aka manta da su a harkokin sadarwa na zamani da suka hada da Intanet, amma suna da wani abin da suke da shi. Na kira su da mutanen da aka manta. Saboda kowa yana tunanin hanyar amfani da hanyoyin sadarwa na zamani amma babu wanda yake batun su "Juakali"."

Africa on the Move Kenia - Videostill
Mai gyaran famfon kichin a gidan Catherine GichungeHoto: DW

"Juakali" kalma ce da ake amfani da ita kan ma'aikatan da suke aiki ba a hukumance ba. Da harshen Swahili tana nufin karkashin rana, saboda galibin ma'aikatan suna aiki cikin rana. Irin wadannan ma'aikata ke tafiyar da mafi yawan tattalin arzikin Kenya. Uku cikin hudu na ma'aikata a kasar suna karkashin wannan tsari. Ba kamar aiki da ke a hukumance ba, babu wata ka'ida ko kariya. Bisa wannan sabuwar hanya ma'aikatan suna da wata damar samun kudin aiki mai inganci, abin da ya fara janyo hankalin mutane. Aly-Khan Satchu masanin tattalin arziki a Kenya ya yi imanin cewa wannan abu zai kawo sauyi:

"Wannan farkon sauye-sauye ke nan. Ina nufin harkokin sadarwa. Me ake nufi a nan? Ina nufi galibin ma'aikata na "Juakali" ba sa da hanyoyin sadarwa. Hada su zai kawo inganci, da samar da aiki ga kowa. Wannan misali kan abin da za a yi, muna ganin sauye-sauye da suke canja hanyoyin da ma'aikata ke aiki."

Yanzu an fara samun sauyi. Shiga hanyar sadarwa da Catherine Gichunge ta kirkiro da ake kira "RedAnt" ga ma'aikata ana bukatar biyan kudaden da suka kai dalar Amirka biyu na rijista sannan kowane wata a biya kimanin Centi 50.