Kenya na shirin daukar sabbin jami′an kiwon lafiya | Labarai | DW | 08.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kenya na shirin daukar sabbin jami'an kiwon lafiya

Hukumomin Kenya sun ce suna shirin yin kira ga jami'an kiwon lafiya na kasashen waje domin maye gurbinsu da na cikin gida da ke yin yajin aiki kusan watanni uku da suka wucce wadanda kuma aka gaza cimma sulhu da su.

A  karo da dama  gwamnatin ta Kenya ta sha yin barazanar korar wasu likitocin tare da kule wasu 'yan kwadago a gidan kurkuku domin tilasta musu da su koma bakin aikinsu.Ma'aikatan na kiwon lafiya na Kenya  wadanda ke bukatar karin kudaden albashi na kuma bukatar a kara samar da kayayyakin aiki a cikin asibitocin na Kenya.