1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya: An yi wa Uhuru Kenyatta kashedi

Suleiman Babayo
September 4, 2017

Kungiyoyin fararen hula na Kenya sun yi kashedi ga Shugaba Uhuru Kenyatta bisa yadda ya ke sukar lamirin kotun koli wadda ta soke zaben shuagaban kasa a watan jiya.

https://p.dw.com/p/2jLCV
Kenia nach der Annulierung der Präsidentenwahl | Uhuru Kenyatta
Hoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

Wannan kalamai sun samu martani mabanbanta daga bangarori daban-daban na Kenya, inda galibi ake caccakar shugaban kan yadda ya dau aniyar saka kafar wando daya da alkalan. Gamayyar kungiyoyin fararen hula na Kenya karkashin Kura yangu sauti yangu sun fitar da sanarwa inda suka bukaci Shugaba Kenyatta ya ba da hakuri bisa kalaman da ya yi duba da irin hadarin da suke da shi.

Guda daga cikin masharhantan Kenya Njonjo Mue ya ce kotun tsarin mulki da ta soke zaben da sauran bangaren shari'a na aiki ne domin kare muradun daukacin mutanen Kenya inda ya kara da cewar ''idan shugaban kasa ya yi barazana ga bangaren shari'a to ya na yi mana barazana ne baki daya, kuma muna shaida masa ya daina haka."

Tuni dai masu ruwa da tsaki a harkar zaben Kenya musamman ma wanda suka sanya ido kan zaben da ya gabata kamar Regina Opondo wadda ta jagoranci 'yan saka ido na cikin gida suka bukaci hukumar zaben kasar ta fitar da jadawalin zaben cikin kankanin lokaci. Haka ma abin ya ke ga ministan ilimi na kasar ta Kenya Fred Matiang wanda kuma ya ke rike da ma'aikatar tsaron cikin gida ya nemi hukumar zaben ta IEBC ta saka lokacin zaben kafin 17 ga watan Oktoba mai zuwa saboda kar a samu matsala bisa jarabawa da dalibai na kasa za su rubuta.