1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya: An dage ranar sake zabe

Abdul-raheem Hassan
September 21, 2017

Hukumar zaben kasar Kenya, ta sanar da dage ranar da za'a sake gudanar da zaben shugaban kasar daga ranar 17 ga watan Oktoba zuwa ranar 26 ga watan Oktoba.

https://p.dw.com/p/2kUYq
Kenia Nairobi nach der Wahl
Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

A wata sanarwa da hukumar zaben ta fitar, ta ce an dage ranar sake shirya zaben ne biyo bayan bayanai mai dauke da tsarkakiya da kotun kolin kasar ta  bayyana kan yadda za'a sake shirya zaben.

Dama dai Kotun kolin kasar ta Kenya, ta bada wa'adin kwanaki 60 don shirya wani sabon zabe, wato ranar 17 ga watan Oktoba. Kotun dai ta soke babban zaben da ya yugadana a watan Agusta bayan da ta zargi hukumar zaben na rashin gabatar da sakamako mai inganci.

Tun dai bayan soke babban zaben, kasar Kenya ke cikin fargabar barkewar rikicin bayan zabe, ganin yadda zafafan kalamai ke ci gaba da fita a tsakanin shugaban kasar Uhuru Kenyata wanda hukumar zaben ta ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben a karon faro, da abokin karawasa Raila Odinga.