1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Keken Chukudu a Kwango

A'Raheem Hassan/ YBOctober 14, 2015

An kirkiro da wani keken katako mai suna Chukudu a Gabashin Kwango, inda a yanzu haka wannan fasahar ke zama ginshikin tattalin arzikin yankin.

https://p.dw.com/p/1Gnkv
Kongo Tschukudu Lasttransporter
Matashi na tuka keken Chukudu a KwangoHoto: Getty Images/AFP/J. D. Kannah

Keken Chukudu dai, a yanzu ya zama gama-gari a yankin Goma. An saba da wannan kekunan katako na daukan kaya kirar Kwango, saboda da sauki wajen dakon kaya masu nauyi daga nesa sannan ga biyan bukata cikin sauri.

Ana dai kera keken Chukudu ne daga katako da ke da karkon gaske, to sai dai akwai bukatar hakuri da juriya, kafin masu fasahar su cimma kera Chukudu mai inganci. Sébastian Pascal daya daga cikin masu kera keken ne, kuma ya gaji aikin ne daga mahaifinsa inda a yanzu yake kera keken Chukudu akan Dala 100 kan ko wane guda.

Bukatar juriya a kera keken

Kongo Tschukudu Lasttransporter
Matasa na daukar dako da keken ChukuduHoto: Getty Images/AFP/J. D. Kannah

"Aikin na bukatar hazaka. To amma abin da ke da wahala a aikin shi ne, yadda zaka sassaki itace sannan ka harhada bangarorin keken har ya zauna daidai."

Ko da yake dai akan samu yawancin bangarorinda ake sarrafa keken Chukudu a yankin Goma. To amma duk da haka,yana daukan akalla kwanaki uku kafinn Paskal da sauran abokan aikinsa su kammala sarrafa keken Chukudu guda daya.

Wannan kekeken dai ba sufurin mutane kadai yake yi ba, ana kuma dakon kaya masu nauyin gaske daga wuraren daban-daban. A don hakanema aka kafa wani mutum-mutumi a shatale-talen tsakiyar garin Goma don girmama wannan kyakkyawan tsarin sufurin keken na Chukudu.

A cikin ra'ayi mabanbanta ne dai, mazauna garin na Goma ke yaba kyakkyawan tsarin keken na katako da a yanzu ya zama abin tinkahon yankin.

Kongo Tschukudu Lasttransporter
Yaro na tuka keken Chukudu a wani titi a Gabashin KwangoHoto: Getty Images/AFP/P. Moore

Da irin wannan namijin kokari na kera keken Chukudu da Paskal ya bullo da shi, a yanzu iyalansa na alfahari da shi matuka, kamar dai yadda wata 'yar uwarsa ta bayyana.

Hausawa dai suka ce bayan wuya sai dadi, a yanzu dai Pascal ya yi amannar cewa aikin hazaka shi ne hanyar samun ci-gaba a Gabashin Kwango mai fama da rikici.