Kawar da muggan makamai | Labarai | DW | 23.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kawar da muggan makamai

Man'yan ƙasashen duniya sun fara ganawa, don ganin an samu duniyar da bata da makaman ƙare dangi

default

Rumbun makaman ƙare dangi na Rasha

Wasu ƙasashe goma masu faɗa aji, sun fara wani taro don kawar da makaman nukiliya a duniya. ƙasashen waɗanda ke taron a ƙarƙashin jagorancin Jamus da Japan da Ostaraliya, suna taron na su ne a gefen inda ake taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle yace, samun duniyar da bata da makaman nukiliya wani mahimmin abune ga muhallin duniya. Inda ya yi gargaɗin cewa, in ba'a ɗau matakai ba, to makaman nukiliya za su iya shiga hannun 'yan ta'adda. ƙasashen goma za su sake ganawa a birnin Berlin a wata ranar da ba'a kai ga bayyanawa ba izuwa yanzu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu