1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kaura tsakanin kasashen kungiyar hadin kan tattalin arziki da raya kasa.

Duk da cewa a cikin shekaru ukun da suka wuce an samu komabayan tattalin arziki a daukacin kasashen kungiyar hadin kan tattalin arziki da raya kasa wato OECD a takaice, kasashe masu arzikin masana´antu na ci-gaba da daukar hankalin baki ´yan ci-rani musamman baki ma´aikata. Alal misali a cikin shekarun 2001 da 2002 kasar Amirka ta ba baki sama da miliyan daya izinin zama na dindindin da kuma yin aiki a cikin kasar. Su ma kasashen Kanada, New Zealand, Switzerland da kuma kasashen kudancin Turai sun dauki baki masu yawan gaske. Amma a kasashen arewacin Turai da kuma Japan yawan bakin ya ragu ne.

Alkalumma sun yi nuni da cewa Jamus na bayan Amirka wajen daukar hankalin baki, sai kasashen Britaniya da Japan. Hakan kuwa ba shi da nasaba da shirin gwamnatin tarayya na ba kwararrun masana ilimin komfuta takardun zama da kuma yin aiki a cikin kasar wato Green Card, inji wani masanin harkar shige da ficen baki na kungiyar OECD, sannan ya kara da cewa hakan bai sa Jamus din ta zama wata kasa da baki ke sha´awar kwarara cikinta ba. Daukacin bakin dake zuwa wannan kasa dai ´yan ci-rani wadanda da zarar kaka ta gama sai su koma kasashensu na asali. Haka zalika baki kadan ne ke shigowa wannan kasar daga wata kasa da ba ta Turai ba. Haka kuma shirin nan na Green Card bai taka wata rawar a zo a gani wajen kwararar baki zuwa wannan kasa kamar yadda aka yi zato ba, inji masanin na kungiyar ta OECD.

Hatta karin yawan bakin a wasu kasashen kungiyar Tarayyar Turai ya samu ne saboda kaura da ´yan kasashen kungiyar EU ke yi zuwa wata kasa ta kungiyar. Sannan kuma an fi samun nasarar shirye-shiryen da ake yi da nufin jan hankalin kwararrun ma´aikata na ketare a kasashen da bisa al´ada suke da dokokin samun walwala ga baki, kamar Amirka da Kanada da Australiya, sai Switzerland da kuma Britaniya a nan nahiyar Turai. Baya ga bakin haure, yawan bakin da ke kwarara zuwa kasashen kudancin Turai na da wani dalili daban, inji masanin na kungiyar OECD. Daukacin baki a wadannan kasashen ba kwararrun ma´aikata ba ne, inda da yawa ke aikin shara ko kwadago a kananan masana´antu. Amma duk da haka akwai kwararrun ma´aikata a fannonin fasahar sadarwa da cinikayya da banki dake kaura zuwa wadannan kasashe.

Har yanzu dai ba´a san irin tasirin da wannan kaura na mutane ke yi a kasashen su na asali ba. Amma duk da haka dai rahoton kungiyar ta OECD yayi bayani game da muhimmanci dake akwai wajen shigar da bakin cikin harkokin yau da kullum na kasashen da suka yi kaura ciki.
 • Kwanan wata 04.02.2004
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvm3
 • Kwanan wata 04.02.2004
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvm3