Katsina: Yaki da zaman kashe wando | Sauyi a Afirka | DW | 25.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sauyi a Afirka

Katsina: Yaki da zaman kashe wando

Wata kungiyar matasa a jihar Katsina ta himmatu wajen ilimantar da matasa, inda a karon farko suka zabo matasa 250 maza da mata suka basu horo na sati uku kyauta da niyyar dakile zaman kashe wando tsakaninsu.

Wadannan matasa dai sun yi hangen nesa ne wajen kafa wannan kungiya ne ganin irin yadda yan uwansu matasa ke zaman kashe wanda babu sana'o'i alhalin kuma akwai damar yin sanao'in yasa suka sadaukar da kansu su na koyar da matasan sana'o'in kyauta a inji jagoran kungiyar Abubakar lawal Mani:

"Kungiya ce mai yaki da talauci da kuma cigaban matasa a jihar katsina, mun duba yanayin zaman takewa ne na rayuwa matasan mu da dama sun gama karatu amma basu da ayyukan yi wasu kuma suna da aikin amma basa zuwa, da akwai da dama wadanda suke bukatar tallafin a koya masu sana'o'in damin su zamo masu dogaro da kai "
 

Shin ko wadan ne irin sana'o'i ne wadannan matasa ke koyar da 'yan uwansu ? Lawal mani ya yi tsokaci

"Da akwai koyar da aikin dinki na maza dana mata dinkin kayayyaki,jikkuna na mata da dinkin jikkuna na yara na makaranta da kuma koyar da aikin sabulu na wanka dana wanki, da Shampoo da Air Freshner"

Kamar nawa zaku kashe wajen wannan aikin?

"To lissafin da muka daiyi ba mai yawa bane amma dai ya kai a kalla naira dubu dari da saba'in da takwas, na kayayyakin aiki kawai da muka saya banda takardu da muka gurza, banda kudin certificate da muka kashe wanda za'a rarraba mawa duk wanda mukaba horo".