1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sauyi a Afirka

Katsina: Matashin da ya samar da ruwan sha

Wani mai tallafa wa al'umma a jihar Katsina ya taimaka wajen samar da ruwan sha kyauta ta hanyar gina fanfunan tuka -tuka cikin unguwanni a garin Katsina, inda kawo yanzu ya gina akalla 27.

Samar da tuka-tuka domin magance matsalar rashin ruwan sha

Samar da tuka-tuka domin magance matsalar rashin ruwan sha

Shi dai wannan bawan Allah ya sha alwashin ci gaba da ba da irin wannan gudunmawa ganin mutane na cikin bukata game da ruwansha ya kuma shaida wa DW dalilinsa na yin wannan aiki. 

"Abubuwan da ke sa hakan ba wani abu bane illa tallafama al'umma saboda zaka ga wasu unguwanni ko akwai yan uwanka koma yayunka saboda haka zaka duk duk yamu yamune." Kamar a unguwarmu nan Wakilin Kudu na samar da akalla guda tara sai wasu wuraren bazan iya kirgasu ba saboda akwai su jefi jefi"

Al'umma da dama dai kan nuna bukatarsu ta neman ruwan sha ga mahukunta dama duk wata hanya da suke ganin in sun bi zasu samu biyan bukatarsu shin ko ta yaya Nadada ke gane masu wannan bukata? Ga abin da yake cewa:

"Ai kaga ni zaunan nan garin nan ne kuma haifaffen nan, saboda haka duk inda keda matsalolin nan yawanci mun sansu, mutane na zuwa muma muna lura sannan akwai mutanenmu da muke zaune dasu wadanda suna jawo hankalinmu da cewar wuri kaza ana neman taimako."

Na shiga irin wadannan Unguwanni da shi Usman Nadada ya samar da irin wadannan hanyoyin ruwan sha domin jin koyaya sukaji da wannan tallafi? Ga bin da suke cewa:

"Sunana Alhaji Abdullahi Haruna Daki Tara munji dadi kwarai da gaske. Alhaji Usman Nadada yana iyaka bakin kokarinsa wajen tallafa wa al'umma musamman yazo yace mu nemi wuri a gina mana wannan rijiya ya." Shi kuwa wannan cewa yake: "Sunana Abdulahi Zagwali ko yau da ruwan da yasa a cikin unguwarmu nai wanka nai alwala, kuma shi ake diba gidajenmu ana hidimar abinci."

Sauti da bidiyo akan labarin