1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katar za ta sayo jiragen yaki daga Birtaniya

Abdul-raheem Hassan
September 17, 2017

Kasar Katar ta amince da yarjejeniyar sayo jiragen yaki 24 daga Birtaniya, sakataren harkokin tsaron kasar kasar Khalid bin Mohammed al-Attiyah da tokoransa Michael Fallon sun rattaba hannu kan yarjejeniyar.

https://p.dw.com/p/2k9CF
Amerikanischer Militäreinsatz in Katar
Hoto: U.S. Air National Guard photo by Master Sgt. Andrew J. Moseley/Released

Wannan yarjejeniya shi ne irinsa na biyu mafi girma da Katar ta cimma a kan harkokin tsaro, tun bayan da kasar ta dau matakan fadada huldar ta a tsakanin kasashe kawayen ta. Ana dai ganin cimma wannan matsaya na sayo jiragen, ka iya dabbaka hulda da kusanci ta kud-da-kud musamman ta fuskar tsaro tsakanin Katar da Birtaniya.

ko da yake dama ana saura kwanaki 10 katar din ta cimma yarjejeniyar ciniki makamai da Amirka, aka samu baraka mai tsanani tsakaninta da sauran kasashen Larabawa da ya kai yanke hulda da ita, bisa zargin tallafawa ta'addanci zargin da Katar din ta sha musantawa.