Kataloniya: Zanga-zangar adawa da kame Puigdemon
March 27, 2018Talla
Hukumomin birnin Barcelona sun ce zanga-zangar ta haddasa tsaiko wajen gudanar da harkokin yau da kullum kamar yadda aka saba, sakamakon toshe manyan titunan birnin da ya haifar da cunkoson ababen hawa.
Tsohon shugaban gwagwarmayar kafa yankin Kataloniyan Carles Puigdemont da ke jiran shari'a a kasar Jamus, ya ce zai ci gaba da fafutukar ganin ya cimma burinsa na samar wa al'ummarsa 'yanci, sannan ya ce jama'ar sa na da 'yancin nuna bukatar samun kasa mai cin gashin kai.