Kataloniya: Tsugune ba ta kare ba | Labarai | DW | 06.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kataloniya: Tsugune ba ta kare ba

'Yan aware na shirin bayyana yancin Kataloniya amma gwamnatin Spain ta ki amincewa.

Gwamnatin 'yan aware na Kataloniya ta ce  al'ummar yankin ta ka'da kuri'ar amincewa da samun yancin kai da kishi 90 ciki dari na kuri'un da aka ka'da a zaben raba gardamar da aka yi ran daya ga watan Oktoba. A ranar Talata dai mai zuwa aka shirya jagoran 'yan aware Carles Puigdemont zai jawabi. Amma kuma gwamnatin Spain ta ce Kataloniya za ta ci gaba da kasancewa cikin Spain