Kasuwar Kirsimeti birnin Köln na Jamus | Zamantakewa | DW | 21.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Kasuwar Kirsimeti birnin Köln na Jamus

Kasuwar kirsimeti wacce aka fi sani da christmas Market a nan kasar Jamus, wata kasuwa ce da take ci duk shekara a cikin watan Disamba kwanaki kadan kafin bikin Kirsimati.

Flash-Galerie Weihnachtsmärkte (picture-alliance/Bildagentur H)

Ita dai Christmas Markt, Tarihi ya nuna cewa kasuwa ce da ta dade tana ci a tarihin kasar Jamus,lokaci ne da 'yan kasuwa daga birane da kauyuka sukan baje hajarsu tun daga safe har dare kuma har ranaikun Asabar da Lahadi,lokaci ne kuma da dubban jama'a suke tururuwa don cin wannan kasuwa kamar yadda bincike ya nuna wasu sukan yi tanadin kudi don cin wannan kasuwa ta christmas Markt mai ci sau daya a shekara. Kasuwar na da wani rin yanayi na nishadi don za ka ga kungiya-kungiya ta samari da 'yan mata ana kwalisa tare da ciye-ciye da shaye-shaye na irin kayan da aka tanada don wannan lokaci. Yara kanana kuwa an yi musu tanadin guraren wasa na shillo na musamma tare da kade-kade. A bangaren daya manya da tsofaffi suma ba a bar su a baya ba a batun cin wannan kasuwa ta kirsimeti kamar yadda wani uba mai suna Harvat ya shaida min cewar cin kasuwar ya zamar masa jiki tunda a shekarun baya 'yarsa yake kawo wa yanzu kuwa jikokinsa yake kawowa:

" Wannan kasuwa ta kirsimeti wato christmas makt gurin nishadi ga yara, su wasanni da jin dadi kafin lokacin kirsimati tare da iyayensu, don haka za su iya zuwa, don ni duk shekara nake zuwa, yauwa ga 'yata nan ta zo da ita nake kawo da kaninta yanzu kuma jikokina na kawo".

Ba wai halartar shagulgulan da ake yi a kasuwar ne yake tara dubban jama'a a gurin ba kawai, domin 'yan kasuwa sukan kawo kayan da ba a faye samun su a kasuwanni ba, sai dai a wannan lokaci kamar yadda wata 'yar kasuwa mai suna Ina mutuniyar Köln ta ce,ta zo kasuwar ne don tallata wasu matassan kai na musamman masu siffar dabbobi wadanda kuma ake gasawa domin jin dumi a lokacin sanyi na Winter.

Flash-Galerie Weihnachtsmärkte 2010 Nürnberg (picture alliance/Bildagentur-online/Forkel)


"Wadannan dabbobi ana saka su a cikin abin dumamma abinci na micro Wave in sun yi dumi sai a yafa a jiki domin maganin sanyi, kuma duk shekara a nan muke zama muna bude shagonmu kuma daga karfe 11 na safe zuwa 9 na dare akullum har Asabar da Lahadi. Ni mutuniyar Köln ce amma a canma haka kasuwar take ci. Wanan abu kuma ana amfani da shi don yin kyauta ga yara ko kowa ma na iya amfani da shi don yafawa a wuya musamman ga tsofaffi ko masu ciwon wuya da an sa a na'urarar dumama abubuwa ta micro-wave ya yi dumi sai ka yafa saboda jin dumi"


Herman wani dattijo ne mai shekaru 54 wanda ke gasa 'yar tsala wacce ake kira da Crepe a harshen Jamusanci a kasuwar, cewa ya yi shi fa don tsananin son da yake wa wannan lokaci na cin kasuwar ta kirsimeti har kyauta yana bayar wa ba sai an saya ba bayan ya gasa ya miko min cikin Annashuwa yana mai cewa:

"Mutane da yawa sun sanni, ungo tabin gishiri. Sama da shekaru 20 nake wannan sana'a a wannan lokaci na christmas markt, sai dai akwai banbanci tsakanin mutanen da suke cin kasuwar yanzu da wadanda suka ci kasuwar a shekarun baya, kowa yana cike da kaunar juna da farinciki, ko da yaushe nakan ba mutane dan kadan, akwai kasuwar kirsimati guda 5 zuwa 6 a garin Köln, amma ban taba zuwa can na yi aiki ba".

Daya gada cikin abubuwan da suke kara wa wannan kasuwa armashi a gurin mutanen Jamus, shi ne wani dandali a gefen kasuwar wanda 'yan mata da samari suke taruwa suna kwankwadar wata barasa da aka tanada musamman dan irin wannan lokaci mai suna gluwine, kamar yadda wani matashi mai suna karson ya ce:

"Christmas mart duk daya ce a ko ina, sannnan wannan abun shan da kike gani a hannuna na musamman ne, minti 10 da suka wuce nazo nan".


A da can ana cin irin wannan kasuwa ce a kusa da babbar cocin kowanne gari saboda jan hankalin jama'a. Daga baya a shekarar 1616 shugabanni suka lura kasuwar na hana jama halartar coci ranar jajiberin chirsimati, daga nan ne suka dauki matakin dauke kasuwannin daga bakin coci-cocin.