Kashin jami′an agaji a Afganistan. | Labarai | DW | 07.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kashin jami'an agaji a Afganistan.

An tabbatar da kashin wasu jami'an agaji a Pakistan.

default

Taswirar yankin Nuristan da ke Afganistan

Wata ƙungiyar ba da agaji mai suna Christian Charity ta ce lallai gawarwakin wasu mutane 10 da aka gano a yankin Nuristan a arewa maso gabashin Afganistan na 'ya'yanta ne. Tun da farko dai akwai saɓanin rahotanni game da asalin waɗanda aka kashen. Sai dai a cewar wannan ƙungiya gawarwakin da aka ganon na wsu ma'aikatanta ne da suka haɗa da Bajamushe ɗaya da ɗan Birtaniya ɗaya da Amirkawa 6 da kuma 'yan Afganistan biyu waɗanda da ke kan hanyarsu ta zuwa Kabul daga garin Nuristan. A sanarwar da ta fitar, Taliban ta ce ta kashe wasu mishan-mishan har guda 10. Yanzu haka dai kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamus ya ce suna tuntuɓar ofishin jakadancinsu a Kabul domin tantance wannan labari mara daɗin ji da aka samu. ƙungiyar ta Taliban ta zargi ƙungiyar agajin da yaɗa addinin kirista, zargin da ƙungiyar ta musanta.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Halima Balaraba Abbas