Kashin farko na karin dakarun Amurka sun isa Iraqi. | Labarai | DW | 15.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kashin farko na karin dakarun Amurka sun isa Iraqi.

Kashin farko na karin dakarun Amurka sun isa kasar Iraqi.

Komandan rundunar Amurka a Iraqi Janar George Casey ya fadawa taron manema labari cewa sojoji 4,000 ne cikin sojoji da Amurka ta shirya karawa karkashin sabbin dabarunta game da Iraqin suka isa kasar.

A halinda ake ciki kuma shugaban kasar Iraqi Jalal Talabani ya isa birnin Damascus na kasar Syria domin tattaunawa da takwararsa Bashar al-Asad.

Wannan itace ziyara ta farko da Talabani zai kai Syria tun bayanda kasashen biyu suka maida huldar diplomasiya a watan nuwamban bara.

Gwamnatin syria ta yanke huldar diuplomasiya ne da Iraqi a 1980 bayan Iraqi din karkashin marigayi Saddam Hussein ta mamaye Iran.

Ana sa ran cewa Talabani da Assad zasu yi anfani da wannan ganawa domin sanya hannu kan yarjejeniyoyin cinikayya da tsaro.

Tun farko dai kasar Amurka ta zargi Syria da gazawar daukar matakan da suka dace wajen dakatar da sojojin sa kai ratsawa zuwa cikin kasar Iraq daga kasarta.

A nata bangare gwamnatin Syria ta karyata wannan zargi.