Kashin farko na dakarun AU sun isa Somalia | Labarai | DW | 01.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kashin farko na dakarun AU sun isa Somalia

Kashin farko na dakarun wanzar da zaman lafiya karkashin kungiyar taraiyar Afrika ya isa birnin Mogadishu na kasar Somalia a yau alhamis.

Babban jamiin yan sanda a kudancin Baidoa inda fadar gwamnatin take Adan Biid Ahmed ya fadawa kanfanin dillancin labaru na AP cewa dakarun kasar Uganda 30 sun isa Baidoa a yau da safen nan inda gwamnan Baidoa da wasu jamian soji suka tarbe su.

Ana sa ran Uganda zata aike da dakarunta kusan 1,500 zuwa kasar ta Somalia.