1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kashedi ga shugaban Guinea Bissau

Salissou Boukari
May 12, 2017

Kwamituin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kashedi ga shugaban Guinea Bissau Jose Mario Vaz da ya yi kokarin nada Firaminista a kasar.

https://p.dw.com/p/2cpx6
Guinea-Bissau Jose Mario Vaz
Shugaban kasar Guinea Bissau Jose Mario VazHoto: Getty Images/AFP/Seyllou

Cikin wata sanarwa da ta samu amincewar dukannin membobin kwamitin 15, Majalisar Dinkin Duniyar ta sanar cewa a shirye kwamitin yake ya dauki dukkannin matakan da suka dace, domin bada amsa ga duk wani yanayi na tabarbarewar lamurra a kasar ta Guinea Bissau. Wannan karamar kasa da ke yankin yammacin Afirkana fuskantar tarin matsaloli da ke da nasaba da rikicin siyasa, tun bayan da shugaban kasar Mario Vaz ya kori Firaministansa Domingos Simoes Pereira a 2015, wanda kuma shi ne shugaban jam'iyya mai mulki ta shugaban kasa.

A watan Nuwamba na 2016 shugaban  ya nada Umaro Sissoco Embalo a matsayin sabon Firaminista, amma kuma jam'iyar PAIGC mai mulki a kasar ta yi watsi da nadin, inda ta zargi shugaban kasar da taka ka'idojin yarjejeniyar da aka cimma tare da kungiyar ECOWAS.