Kashe yara ƙanana biyar a Jamus | Labarai | DW | 07.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kashe yara ƙanana biyar a Jamus

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kira taron maganta matsaloli na cikin ƙasa adangane da kulawa da yara kanana,sakamakon wasu yara ƙanana maza guda 5 da iyayensu masu taɓin hankali sukayi.Mataimakin kakakin gwamnati Thomas Steg ya fadawa manema labaru a birnin Berlin cewar,gwamnati tana cikin bakin cike da bacin rai dangane da wannan matsala.Yace ayar tambaya dai itace,ko gwamnati na taka rawar data kamata ,kuma hakan nayin tasiri?Taron wanda zai gudana a ranar 19 ga watan Disamba,zai samu halartan dukkan Premiyoyin jihohi da ministocin kula da harkokin iyalai dake jihohi 16,dake nan tarayyar Jamus.A ranar laraba nedai jamian yansanda suka tsinci gawarwakin yara biyar kuma ‚yan uwan juna ,wadanda shekarunsu ke tsakanin 3-9,a wani gida dake kauyen Darry,wadda mahaifiyarsu tace ita ta kashe su, sakamakon tabun hankali da take fama dashi.