KASHE KASHEN YAN JARIDA A 2003 | Siyasa | DW | 06.01.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

KASHE KASHEN YAN JARIDA A 2003

Rahotanni da wasu kungiyoyi biyu suka fidda na nuni dacewa shekarata 2003,na mai zama bakin shekara wa yan jarida,wanda ya kasance mafi munin irinsa a kusan shekaru 10 da suka gabata.Rahotan kungiyar kare hakkin yan jarida ta Reporters without Borders dake da zama a birnin Paris da Komititin kare yan jarida mai matsuguni a birnin New York,ya bayyana wahalhalun da yan jarida suka kasance ciki a shekarar data gabata. Kungiyar ta faransa ta bayyana sunayen yan jarida 42 da akayiwa kisan gilla a bara kadai,ayayinda takwararta a wani rahoto daban tayi nuni da yan jarida akalla 36 da suka rasa rayukansu.Kungiyoyin biyu sun bayyana cewa yawan yan jarida da suka mutu a bara ya ninka na shekarata 2002,abunda suka danganta da yakin kasar Iraki. To a hannu guda kuma rahotannin na nuni da yadda aka tozartawa yan jarida,turasu kurkuku tare da rufe kafofin yada labaru masu zaman kansu,abunda suka danganta da sabbin dokoki da matakai da gwamnatoci suka kirkiro ,a bangaren gudummowansu na yaki da taaadanci da Amurka kewa jagoranci bayan harin 11 ga watan satumban 2001. A kasar Iraki,Yan jarida 19 aka kashe,13 daga cikinsu ta hanyoyi munana,abunda kedada tabbatar dacewa har yanzu Iraki na mai zama wurin barazana ne bawai wa yan jaridan kasashen waje ba,amma harda mazauna cikin wannan kasa. Yakin daya fara tun a watan maris ya kasance barazana wa yan jarida,to sai dai har ya zuwa yanzu bayan yakin,yan jarida dake aiki a kasar na cewa Irakin na mai zama wuri mawuyaci na aiki.Directar komitin Ann Cooper ta bayyana cewa tana mai matukar bakin cikin ganin yadda aka kashe wasu yan jarida 4 sakamakon halayyar Sojin Amurka a Iraki,inda tace kungiyarta har yan na neman cikakken bayani daga hukumar Pentagon ta Amurkan.Bugu da kari Repoers without Boders a nata bangare ta zargi Sojin Amurkan da kashe yan jarida guda biyar a Iraki,wanda har yanzu Amurkawa basu gudanar da wani bincike kann wannan batu ba. Kungiyar ta kumas danganta wannan hali da yan jaridan ke fadawa da amfani da ake karayi da makamai na zamani,ba tare da laakari da irin horo da ake bawa yan jarida ba.Wadannan makamai injita basu damu da kare yan jarida ba,face yin kokarin samun nasaran yaki da suka sanya gaba. Kungiyoyin kare hakkin yan jaridan biyu sun amince dacewa,yawan yan jarida da suka rasa rayukansu a Iraki shine mafi yawa a kasa guda, bayan yan jarida 24 da suka gamu da ajalinsu a Algeria a dauki ba dadi tsakanin da masu tsattsauran raayin addini a shekarata 1995.A wannan shekara kadai yan jarida 49 suka rasa rayukansu.wasu kashe kashen na yan jarida banda na kasar iraki sun hada da wasu biyu da sojin Izraela suka bindige cikin rikicinsu da palasdinwa shekaru 3 da suka gabata,ya zuwa yanzu babu wani mataki da aka dauka kann wannan batu,a Philipines yan Jarida biyar aka kashe bayan sun halarci wani taron kalubalantar rashawa a tsakanin jamian gwamnati,kana a Columbia guda uku akayiwa kisan gilla,kana na hudu aka bindige shi.Bugu da kari a Rasha an dabawa babban Editan wata jarida mai zaman kanta dake yayta ratanni irin badakallan da gwamnati keyi da miyagun ayyukanta ,wuka acikin gidansa,kana aka kashe wanda ya gaji wannan matsayi nashi.Sauran kasashe sun hada da Nepal,indonesia,India,Iran,Cambodia,Burma,Cotedivoire da Guatemala. A bangaren kurkuku kuwa yan jarida kimanin 124 ke tsare,daga cikin 766 da aka kama a bara.A Cuba akwai yan jarida 30,Burma 17,Eritrea 14 kana Iran 11 a tsare a kurkuku.Bugu da kari kafofin yada labaru da dama sun kasance rufe saboda ruwaito rahotaannin dake kalubalantar miyagun ayyukan gwamnatoci.
 • Kwanan wata 06.01.2004
 • Mawallafi ZAINAB AM ABUBAKAR
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvml
 • Kwanan wata 06.01.2004
 • Mawallafi ZAINAB AM ABUBAKAR
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvml