Kashe kashe a Iraki | Labarai | DW | 29.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kashe kashe a Iraki

Yan sanda da wasu majiyoyi na siyasa a Iraki sunce dakarun Iraqi da na Amurka sun kashe sojin sa kai kusan 300 cikin dazuka dake kusa da birnin Najaf.

Gwamnan lardin yace tuni dai sojin sa kai suka shirya kai hari kann shugabannin yan shia a yau litinin,yayinda masu ziyara suke taruwa a birnin don bikin Ashura.

Jiragen saman yaki na Amurka sun kai hari kann yankunan da a cewarsu sojin sa kai suke boye,hakazalika rundunar sojin Amurkan ta sanarda harbo wani jirginta mai saukar angulu,inda mutane biyu dake ciki suka halaka.

Rahotanni dai sunce ana ci gaba da fafatawa.