1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Yamma sun kai hare-hare a Siriya

Salissou Boukari
April 14, 2018

Amirka, Britaniya da Faransa sun aiwatar da kai hare-hare a kasar Siriya kaman yadda suka sha nanata cewa za su yi hakan a wani mataki na mayar da martani ga gwamnatin Shugaba Bashar Al-Assad.

https://p.dw.com/p/2w2Si
Zypern Kampfjet nach Einsatz
Daya daga cikin jiragen yakin kasashen YammaHoto: picture-alliance/AP Photo/P. Karadjias
USA - Trump ordnet Militärschlag auf Syrien an
Shugaban Amirka Donald TrumpHoto: picture-alliance/dpa/AP/S. Walsh

Kasashen sun kai wannan hari ne bayan da suka ce suna da tabbacin cewa gwamnatin ta Siriya ce ta kai harin makami mai guba a birnin Douma da ke yankin Gabashin Ghouta zargin da Rasha da Siriya suka sha musantawa. Shugaban kasar Amirka Donald Trump ya yi jawabi, inda ya sanar cewa ya bada  umarni a kai harin inda yake cewa: "Na baiwa sojojinmu na Amirka izini na su kai hare-hare kan mahimman wurare a kasar ta Siriya domin mayar da martani kan matakan da Shugaba bashar Al-Assad ya duka na kai hari da makamai masu guba kan 'yan kasarsa. Kuma wannan hari kasashen Faransa da Britaniya suma sun shiga an yi tare da su kuma ina isar da godiyata a gare su."

A cewar babban farsan hafsoshin kasar ta Amirka Janar Joe Dunford, sojojin kasashen yamma sun kai hare-hare da misalin karfe daya na dare ga wasu mahimman wurare uku da ake ajiye da makamai masu guba. daya kusa da birnin Damas, sannan biyu a yankin birnin Homs da ke tsakiyar kasar ta Siriya.

Wani dan jarida na kamfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP, ya ce sun ji karan fashewar ababe da kuma karan jiragen yaki tare da tirnikewar hayaki a yankin Arewa maso gabashin birnin Damas. Tuni dai kungiyar Tsaro ta NATO cikin wata sanarwa da sanyin safiyar wannan Asabar din ta ce ta goyu bayan wannan hari da Amirka, Faransa da kuma Britaniya suka kai a Siriya.

Syrien Damaskus Militärschlag
Birnin Damas lokacin da aka kai hari da tsakiyar dareHoto: Imago/Xinhua/A. Safarjalani

Rasha ta ce kasashen sun jefa makamai masu lizzami sama da 100, amma kuma da dama daga cikinsu makamman bada kariya na kasar Siriya sun  kakkabosu. Gidan talbijin din kasar ta siriya ma dai ya sanar da rawar da makamman bada kariya na kasar suka taka wajen kakkabo da dama daga cikin makaman da aka harbo musamman a yankin birnin Homs. Ministan harkokin tsaron kasar ta Rasha ya sanar cewa, hare-haren da Amirka, Faransa da Britaniya suka kai bai taba ko kusa da inda sojojin kasar ta Rasha suke na sama ko na ruwa a kasar ta Siriya ba, inda yace babu wani makami mai lizzami daya da ya rabi wuraran da Rasha ke sa ido a kasar ta Siriya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya yi kira ga kasashen da ke da ruwa da tsaki kan rikicin kasar ta Siriya da suka kai zuciya nesa tare da kaucewa duk wani abu da ka iya kara ta'azzara wannan rikici bayan hare-haren da sojojin suka kai a Siriya. Sakaraten na MDD ya dage bulaguron da ya yi niyar yi a kasar Saudiyya, domin kula da abun da ka iya biyo bayan hare-haren da kasashen Amirka, Faransa da Britaniya suka kai a kasar ta Siriya.

Syrien Damaskus Proteste nach Militärschlag
'Yan kasar Siriya na zanga-zanga kan harin da kasashen Yamma suka kaiHoto: Reuters/O. Sanadiki

Kasar Iran da ke a matsayin mai marawa kasar ta Siriya baya, ta yi Allah wadai da hare-haren da kasashen suka kai a Siriya, inda ta yi kasheidi kan kalubalen da ka iya biyo bayan wannan mataki. Daga nata bangare Isra'ila cewa hare-haren da Amirka, Faransa da Britaniya suka kai ya dace ganin yadda gwamnatin ta Siriya ke ci gaba da hukunci na kashe-kashen 'yan kasarta da makami mai guba.