Kasashen yamma na neman hana cinikin fasahohi da Iran | Labarai | DW | 24.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen yamma na neman hana cinikin fasahohi da Iran

Kasashen Amurka Faransa da Burtaniya suna neman komitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya haramta sayarda makamai masu linzami da fasahar nukiliya ga kasar Iran tare da kawo karshen yawancin shirye shiryen taimakon fasahohin zamani na hukumar kare yaduwar makaman nukiliya a Iran.

Jamian diplomasiya na majalisar dinkin duniya wadanda suka nemi a boye sunansu sun baiyana cewa,wannan shawarar zata bukaci sauran kasashe membobi na majalisar da su hanawa jamian kasar Iran wadanda suke da hannu a shirinta na nukiliya shiga kasashensu .