1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Turai suna ci gaba da Allah wadai da kalaman shugaban Iran

December 9, 2005
https://p.dw.com/p/BvHE

Kasar Rasha ta shiga sahun kasashen turai dake Allah wadai da kalaman shugaban kasar iran Mahmud Ahmedinejad,cewa kamata yayi a a mayarda kasar Israilan nahiyar turai,tare kuma da shakku da yanuna game da kisan kiyashi da akayiwa yahudawa a likacin yakin duniya na 2.

Shugaban na Iran wanda ya fadi a watan oktoba cewa kamata yayi a kawadda Israila daga taswirar duniya,yace,idan har kasashen jamus da Austria sunyi imanin cewa an kashe miliyoyin yahudawa to kamata yayi su samar mata da kasa a yankunansu.

Kasashen Austria,Jamus Israilan kanta da Amurka sun fito sunyi suka da kakkausar murya wannan kalami na Ahmedinajad.

A yau din nan ne maaikatar harkokin wajen Austria tayi sammacin jakadan Iran a Austria,inda ta baiyana masa rashin jin dadinta game kalamin na shugaban Iran,da kuma cewa Israila halartacciyar kasashe ce da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa ta.

Haka itama majalisar yahudawan Jamus ta bukaci kasar jamus da ta yanke huldar jakadanci tsakaninta da Iran saboda wannan kalami da yayi.