kasashen Turai sun yi maraba da tayin da Amurka ta gabatar kan Iran | Labarai | DW | 01.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

kasashen Turai sun yi maraba da tayin da Amurka ta gabatar kan Iran

Kasashen Faransa da Jamus da kuma Biritaniya , sunyi maraba da tayin da Amurka tayi na shiga shawarwari na kai tsaye a game da shirin Iran na mallakar makamin nukiliya, matukar Iran din ta dakatar da aniyar ta na ci gaba da sarrafa sanadarin Uranium..

Kasashen na kungiyyar tarayyar Turai dake gudanar da wani taro a can birnin Vienna na kasar Austria, a game da wannan batu, sun ce suna fata mahukuntan na Tehran zasu gane muhimmancin sauyin wannan manufa daga kasar ta Amurka.

Wannan dai shine karon farko a tsawon shekaru da dama da kasar ta Amurka ta nuna amannar tattaunawa ta kai tsaye da kasar ta Iran.

A lokacin da take maraba da wannan mataki na Amurkan , kasar Sin bukatar Amurkan tayi da kada ta gindaya wasu sharudai na shiga zauren tattaunawar sulhun.

Ya zuwa yanzu dai ba wani martani a hukumance da mahukuntan na Iran suka mayar a game da wannan batu.