1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Sin da Rasha na adawa ga shawarar matsa wa Iran lamba a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Ɗuniya.

March 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bv50

Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya yi zamansa na farko a kan batun makamashin nukiliyan Iran. Rahtoannin da suka iso mana daga birnin New York sun ce Birtaniya da Faransa, tar da goyon bayan Amirka, sun gabatad da wani ƙuduri, wanda zai bukaci a miƙa wa kwamitin rahoto, kan irin ba da haɗin kan da Iran ke yi ga bukatun da ake yi mata na ta soke duk wasu shirye-shirye na sarrafa yureniyum. Sai dai, rahotannin sun ce Rasha da Sin sun sanya alamun tambayoyi kan matakin da Birtaniya da Faransan ke son a ɗauka. Jakadan Sin a Majalisar Ɗinkin Duniya, Wang Guangya, ya faɗa wa maneman labarai cewa, ƙasarsa na da matsala wajen amincewa da shwarar. Sin dai, inji shi, ta fi gwammacewa ne da a bai wa Hukumar kula da Makamashin Nukiliya ta Ƙasa da Ƙasa, watto IAEA, isasshen lokaci don ta iya sasanta rikicin ta hanyar diplomasiyya. Ana dai sa ran kwamitin sulhun zai ci gaba da tattauna wannan batun a cikin wannan makon.