Kasashen Sin da Rasha ba sa goyon bayan takunkumi akan Iran | Labarai | DW | 17.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen Sin da Rasha ba sa goyon bayan takunkumi akan Iran

Kasashen Rasha da Sin sun baiyana a yau karara cewa,basa goyoyn bayan lakabawa kasar Iran takunkumi domin tilasta mata dakatar da shirinta na nukiliya,inda suka ce har yanzu hanyar tattaunawa a bude take.

Wannan kalami nasu kuwa ya baiyana irin farraga dake tsakanin manyan kasashen duniya akan batun Iran.

Yanzu haka dai hukumar sa ido akan yaduwar makaman nukiliya ta kasa da kasa tace,zata gudanar da wani taron gaugawa domin tattauna batun a ranar 2 ga watan fabrairu mai zuwa.

A halin da ake ciki kuma wakilin kasar Iran a hukumar kare yaduwar nukiliya,Ali Asgar Soltaniyeh yace kasarsa ba zata dakatar da aiyukanta na nukiliya ba kuma zata janye dukkan wani hadin kai da take baiwa masu binciken nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya,muddin dai an kaita gaban komitin sulhun.