Kasashen Sin da koriya ta kudu sun soki lamirin kasar Japan.. | Labarai | DW | 15.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen Sin da koriya ta kudu sun soki lamirin kasar Japan..

Kasashen sin da koriya ta kudu sun bayyana takaicin su ga kasar Japan, bisa wata ziyara da Faraministan kasar wato Junichiro Kuizumi ya kai izuwa gurin ibada na yasukuni.

A cewar ma´aikatar harkokin wajen sin, wannan ziyara babu shakka zata shafi tushen dangantakar dake akwai a tsakanin kasashen biyu.

Ita kuwa koriya ta kudu cewa tayi zata aikewa da jakadan na Japan a kasar takardar sammace don nuna masa bacin ransu a fili a game da wannan abu.

A cewar kasashen biyu shugaban na Japan bai yiwa duniya adalci ba, a game da wannan karramawa da yayiwa mamatan.

Wannan gurin ibadar dai, na dauke ne da miliyoyin yan Japan da suka rasa rayukan su, a lokacin yakin duniya na 2 , ciki har da sojojin kasar da aka same su da laifuffukan yaki.

Rahotanni dai sun nunar da cewa wannan ziyara ta Kuizumi tazo ne a dai dai lokacin da kasar ta Japan ke bikin yin saranda a lokacin yakin duniya na biyu a shekara ta 1945.