kasashen Musulmi na taro a Istanbul | Labarai | DW | 12.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

kasashen Musulmi na taro a Istanbul

Shugaban kasar Turkiya Racep Tayyip Erdogan ya tarbi Sarki Salman na Saudiyya domin tattauna dangantakar harkokin kasuwanci a gabanin taron kungiyar OIC.

Ziyarar Sarki Salman na Saudiyya na zuwa ne a daidai lokacin da ministocin kungiyar kasashen Musulmi ta duniya OIC ke gudanar da wani taro a Istanbul.Sarki Salman na Saudiyya tare da tawagarsa za su gudanar da wasu jerin tattaunawa kafin daga bisani su wuce kai tsaye babban taron OIC da ake gudanarwa yanzu haka a birnin Istanbul.

A yayin fara taron sai da ministan harkokin wajen Turkiyan Mevlut Cavusoglu ya shaidawa duniya cewar: "A matsayinmu na al'ummar Musulmi a duniya lokaci yayi da ya kamata mu dakatar da abubuwan da ke faruwa a Syriya, ya zama wajibi mu yi duk abin da ya dace wajen dawo da zaman lafiya a Siriya, kana a fili take sauyin da ake bukatar samu ba zai yiwu ba a gwamnatin Bashar al-Assad."