kasashen larabawa sun bukaci hanyoyin diplomasiyya don warware rikicin Nukiliyar kasar Iran | Labarai | DW | 19.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

kasashen larabawa sun bukaci hanyoyin diplomasiyya don warware rikicin Nukiliyar kasar Iran

Kasashen larabawa dake yankin Gulf sun bukaci tattaunawa ta diplomasiya a game da takaddamar nukiliya tsakanin Iran da kasashen yammcin turai. An ruwaito Sakataren kungiyar kasashen na yankin Gulf Abdulrahman al – Attiyah na cewa tattaunawa ta fuskar diplomasiyya ita ce kadai masalaha ta warware takaddamar. A cikin wannan watan ne dai Iran din ta koma cigaba da sarrafa sinadarin ta na Uranium bayan da aka gabatar da ita a gaban kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya. Kasashen yamma musamman kasar Amurka na zargin cewa Iran nada burin kera makamin Nukiliya, to amma Iran ta musanta wannan batu da cewa shirin ta na Nukiliya na lumana ne.