Kasashen komitin sulhu sun amince a kai Iran gaban komitin. | Siyasa | DW | 31.01.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kasashen komitin sulhu sun amince a kai Iran gaban komitin.

Zaunannun membobi 5 na komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya,sun amince a yau din nan cewa,ya kamata hukumar kare yaduwar nukiliya ta mika masa matakan da dole zata bi,domin bada hadin kanta ga hukumar.

default

Ministocin harkokin wajen kasashen,Sin,Rasha,Amurka,Faransa da Burtaniya,Jamus da Kungiyar Taraiyar Turai,bayan liyafar cin abincin dare a birnin London,sun baiyana cewa,dole ne hukumar kare yaduwar makaman nukiliya ta kasa da kasa ta yanke shawarar mika batun Iran gaban komitin,a lokacin taronta ranar alhamis a Vienna.

Sanarwar da suka fito da ita,ta bukaci hukumar data mika shawarwarinta game da matakan da ake bukatar Iran ta dauka game da wannan batu.

Wani babban jamiin kasar Amurka yace,wannan sanarwar ta nuna cewa, kasashen Sin da Rasha,sunbi sahun Amurka da Kungiyar TaraiyaTurai,cewa,dole ne hukumar kare yaduwar makaman nukiliya ta dauki tsauraran matakai na hana Iran kera makaman nukiliya.

Sai dai kuma wannan yarjejeniya,ta amince da bukatar kasar Rasha,ta dakatar da daukar matakai da suka hada da takunkumi akan Iran,har sai bayan taron hukumar a watan maris.

Ministocin sun bukaci komitin,da ya jira rahoton hukumar,wanda ake sa ran Darekta Janar Muhammad al Baradei zai mika wajen taron nata na watan maris,kafin ta dauki wani mataki,sai dai kasar Amurka tun farko ta so darektan ya mika rahotan nasa wajen taron wannan mako.

Amurka da sauran mukarrabanta dai suna ganin cewa,Iran na kokarin kera makaman nukiliya ne,batu kuma da Iran din ta karyata,tana mai nanata,yancinta na samun fasahar nukiliya,ta kuma tsorata kasashen yammacin duniya bayan komawarta binciken nukiliya.

Duk da cewa,komitin sulhun ya baiwa hukumar kare yaduwar nukiliya umurnin mika Iran din gabansa,sanarwar daya bayar,bata baiyana abinda komitin zai yi ba,idan ya samu rahoton a gabansa.

Ministan harkokin wajen Burtaniya,Jack Straw,ya baiyana cewa,ministocin suna da raayi iri guda game da shirin nukiliya na Iran,inda yace,ana bukatar samun tabbaci na tsawon lokaci daga Iran kafin a amince da ita.

Komitin sulhun dai zai iya lakabawa Iran takunkumi,sai dai akwai wasu matakai da zai iya dauka kafin a kai ga takunkumin.

Kasar Rasha tun farko ta shawarta cewa,hukumar kare yaduwar nukiliya zata bukaci komitin sulhun ya tattauna batun Iran,sannan ya sake mika ta ga hukumar.

Ministocin sun sake kira ga Iran ta dakatar da binciken nukiliya,inda suka amince tsakaninsu cewa,ya kamata su ci gaba da bin hanyoyin diplomasiya domin kawo wannan takaddama.

A jiya litin Iran ta mika wasu shawarwarinta ga jamian Kungiyar Taraiyar Turai da suke taro a Brussels,inda suka baiyana mata cewa,sake komawa taburin muhawara da kasashen turai ya dogara ne akan amincewar Iran da bin bukatun hukumar kare yaduwar nukiliya na kasa da kasa.

 • Kwanan wata 31.01.2006
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu21
 • Kwanan wata 31.01.2006
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu21