1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen gabashin Afrika suna fuskantar matsananciyar yunwa

Hauwa Abubakar AjejeJanuary 2, 2006

A jawabansu na sabuwar shekara,shugabannin kasashen gabashin Afrika,sun baiyana cewa miliyoyin jamaar yankin ne suke fuskantar matsananciyar yunwa saboda rashin isasshen ruwan sama da ya shafi noma da kiwon dabbobi a yankin

https://p.dw.com/p/Bu2q
Hoto: AP

Shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki,yace bala’in yunwa dake fuskantar yankin gabashin Afrika,wata masifa ce ga yankin,inda ya baiyana cewa akalla kashi 20 cikin dari na jamaar kasarsa miliyan 32, zasu bukaci taimakon abinci daga ciki da wajen kasar.

Yace nan da watanni 6 masu zuwa,mutane miliyan biyu da rabi na kasar zasu bukaci agajin abinci,inda yace zaa bukaci kimanin dala miliyan 152 don magance wannan matsala da take fuskantarsu.

A halin da ake ciki yanzu,akalla mutane 20 da kuma daruruwan dabbobi suka halaka,sakamakon fari da matsancin karancin abninci a kasar ta Kenya.

A karamar kasar Burundi mai arzikin koffee kuma shugaba Pierre Nkurunziza,ya rage haraji akan kayaiyakin abinci da ake shigowa da su,domin taimaka ciyarda dubban manoma dake yankunan karkara.

A sakonsa na sabuwar shekara Nkurunziza,tsohon madugun yan tawaye da aka zaba shugaban kasa a watan Agusta yace,saboda yunwa da ke addabar wasu sassa na kasar,daga yanzu gwamnati ta yanke shawarar rage harajin da ta dorawa kayaiyakin abinci take shigo da su daga kashi 30 zuwa kashi 5 cikin dari.

Ya kuma sanarda sakin fursunoni wadanda suka kamala kashi daya bisa 4 na yawan watanni da aka yanke musu a gidajen yari,don rage cunkoso a gidajen yari na kasar, kodayake wannan ahuwa bata shafi masu laifukan fyade da kisan kai ba.

Amma yayi alkawarin sake fursunonin siyasa nan bada jimawa ba,bayan hukumar daya kafa ta duba batun sake fusunonin ta kamala aikinta.

Kasar Burundi dai tana farfadowa ne daga shekaru 12 na rikici tsakanin yan kabilar Hutu da Tutsi,wanda yayi sanadin mutuwar akalla mutane 300,000.

A makwabciya Tanzania kuma,sabon zabebben shugaban kasa, Jakaya Kikwete,ya baiyana damuwarsa da halin rashin abinci da kasar take ciki,inda ya bukaci jamaarsa da su kula da dan abinci da suke da shi.

Yace an samu karancin ruwan sama a yankunan da daman na kasar ta Tanzania saboda haka a cewarsa ya kamata mutane su san yadda zasu yi tattlin abincin da suke da shi yanzu.

Kikwete wanda aka rantsar da shi a ranar 21 ga watan disamba da ya gabata,ya nuna damuwarsa game da farashin kayan abinci da yayi tashin gwauron zabi sakamakon fita da abinci da akeyi daga kasar zuwa kasashen Zambia da Malawi ba tare da sa idon gwamnati ba.

Gwamnatin tace,mutane 613,000 ne zasu bukaci taimakon ton 21,5000 na abinci daga yanzu zuwa watan fabrairu mai zuwa,amma yace akwai yuwuwar karuwar wannan adadi saboda rashin wadataccen ruwan sama.

Hukumar kula da sanarda bullar balain yunwa cikin gaugawa dake da zama a Amurka,tun farko tayi gargadin cewa,miliyoyin mutane a kasashen Habasha da Somalia suna fuskantar matsannancin karancin abinci sakamakon rashin ruwan sama a wadannan kasashen.