1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Kasashen G7 za su kakabawa Iran takunkumi saboda Isra'ila

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 18, 2024

Kasashen na G7 sun hada da Amurka da Burtaniya da Faransa da Japan da Canada, sai Jamus da kuma Italiya

https://p.dw.com/p/4euAv
Hoto: Olivier Douliery/AP Photo/picture alliance

Ministocin harkokin waje na kungiyar kasashen G7 masu karfin tattalin arzikin masana'antu a duniya, za su gudanar da wani taron gaggawa a wannan Alhamis, don tattaunawa kan takunkumin da za su kakabawa kasar Iran, sakamakon harin da ta kai wa Isra'ila, tare da dakile fantsamar rikicin Gabas ta Tsakiya.

Karin bayani:Kungiyar G7 za ta ci gaba da taimaka wa Ukraine

Haka zalika ministocin za su tattauna kan yadda za su kara tallafawa Ukraine da makamai, don kare kanta daga mamayar da Rasha ke ci gaba da yi mata, musamman ma bayan wasu munanan hare-hare na baya bayan nan da ta kai wa Ukraine din.

Karin bayani:Taron ministocin harkokin wajen G7 zai mayar da hanakali kan rikicin Isra'ila da Hamas

Za su kammala taron ganawar a ranar Juma'a, wanda zai samu halartar sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg da kuma ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba, inda suka yi kira ga Iran da Isra'ila da su dakatar da duk wani shiri na far wa juna.

Kasashen na G7 sun hada da Amurka da Burtaniya da Faransa da Japan da Canada, sai Jamus da kuma Italiya.