1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Eu sun yi watsi da shawara Britania a game da assusun kungiyar

December 6, 2005
https://p.dw.com/p/BvHm

Kasashen kungiyar gamayya turai, na ci gaba da bayyana ra´ayoyi kan shawara da Britania ta bada, a game da batun kassafin kudin kungiyar EU na shekara ta 2007 zuwa 2013.

Jiya ne Britania ta bayyana wannan shawara, da ta kunshi mahiman matakai guda 3.

Wato rage yawan kudaden assusu baki daya daga shekara ta 2007 zuwa 2013.

Rage yawan kudaden tallafi ga sabin kasashe membobin EU da kuma amincewar Britania na yafe Euro billiar 8 daga jimmilar kudaden da ta ke samu daga wannan assusu.

Ba dawata wata ba sabin kasashen membobin EU su ka yi watsi da wannan shawara.

Haka zalika, kasar Fransa da majalisar kungiyar da hukumar zartaswa baki daya sun bayana rashin gamsuwa.