Kasashen duniya sun yi maraba da amincewa da kundin tsarin mulkin Iraki | Labarai | DW | 25.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen duniya sun yi maraba da amincewa da kundin tsarin mulkin Iraki

Kasashen duniya sun fara tofa albarkacin bakinsu dangane da amincewa da sabon kundin tsarin mulkin Iraqi. Kungiyar tarayyar Turai ta yi lale marhabin da amincewa da tsarin mulkin da masu zabe a Iraqi suka yi sannan a lokaci daya ta yi kira ga ´yan Iraqi da su fito kwansu da kwarkwata don kada kuri´a a zaben ´yan majalisar dokoki da ake shirin gudanarwa a cikin watan desamba mai zuwa. Sakataren harkokin wajen Birtaniya Jack Straw, wanda kasarsa ke rike da shugabancin kungiyar EU a yanzu, ya ce amincewa da tsarin mulkin wani muhimmin mataki ne wajen wanzuwar demukiradiya da zaman lafiya a Iraqi. To amma MDD ta ce ko da yake ta yi maraba da sakamakon amma zaben ya nunar a fili irin sabanin dake tsakanin al´umomin kasar ta Iraqi. A yau dai ne hukumar zaben kasar ta ba da sakamakon kuri´ar raba gardamar da aka gudanar a ranar 15 ga wannan wata na oktoba. Sakamakon ya nuna cewa kashi 78 cikin 100 na masu zabe sun yi na´a da tsarin mulkin yayin da kashi 21 cikin 100 suka yi fatali da shi.