Kasashen duniya na aikewa da sakon fatan alheri ga Mr sharon | Labarai | DW | 05.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen duniya na aikewa da sakon fatan alheri ga Mr sharon

Shugabannin kasashen duniya naci gaba da aikewa da sakon fatan alheri na samun lafiya ga faraministan Isrela, wato Mr Ariel Sharon.

Sakon fatan alherin dai ya biyo bayan halin da sharon ya samu kansa a ciki ne, bayan tiyata da aka yi masa a daren jiya laraba wayewar garin yau alhamis.

Daga dai cikin wadan nan shugabanni akwai Faraminista Silvio Berlusconi na Italiya da Jacques Chirac na Faransa da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Ragowar sun hadar da Shugaba Bush na Amurka da sakataren Mdd Kofi Anan da Faraministan Japan Junichiro Koizumi da kuma kungiyyar tarayyar turai wato Eu.

Wannan rashin lafiya dai ta Sharon, a yanzu haka ta jefa harkokin siyasa a yankin Gabas ta tsakiya, musanmamma a tsakanin kasar da yankin Palasdinawa a cikin wani hali na kaka ni kayi.