Kasashen Burtaniya da Faransa sun amince da aika sojojinsu Kongo | Labarai | DW | 06.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen Burtaniya da Faransa sun amince da aika sojojinsu Kongo

Kasashen Burtaniya da Faransa sun baiyana goyon bayansu ga batun aikewa da dakarun Kungiyar Taraiyar Turai da zasu marawa na Majalisar Dinkin Duniya baya a kasar Kongo.

Kasashen 2 sun baiyana hakan ne a yau kafin taron ministocin kungiyar wadanda suke dari dari da aikewa da sojojinsu zuwa kasar dake cikin rikici a kahon Afrika.

Sakataren tsaro na Burtaniya John Reid da takwaransa na Faransa,Mishelle Alliot Marie, cikin wata takarda da suka sanyawa hannu sun ce ya kamata kungiyar ta amince da bukatar da majalisar ta mika mata na bada dakarunta zuwa aiyukan zaman lafiya a Kongo a lokacin zaben kasar.

Ministocin dai sun fara taruwa a kasar Austria domin gudanar da wani taro na kwanaki 2 da ake sa ran zai duba batun kebe wani bangare na kasafin kudin tsaron kasashen kungiyar wajen gudanar da bincike na hadin kai,yunkuri da masu suka suke ganin barazana ce ga manufofin harkokin sojin yanki.

Taron zai kuma duba yiwuwar kara taimakon aiyukan zaman lafiya na Afrika a Sudan.