kasashen APEC sun yi alkawarin farfado da shawarwarin Doha | Labarai | DW | 19.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

kasashen APEC sun yi alkawarin farfado da shawarwarin Doha

Shugabannin kasashe 21 na kungiyar raya tattalin arziki Asia da kuma Pasifik sun ci alwashin farfado da tattaunar da ta ci tura na kungiyar ciniki ta duniya. A kudirin da aka cimma wanda shugabannin suka sanyawa hannu a karshen taron yini biyu da suka gudanar a Hanoi babban birnin kasar Vietnam, shugabanin sun yi kashedin cewa rushewar shawarwarin Doha wanda ya ci tura a watan Yulin da ya gabata, ba zai haifar da alfanu ga cigaban harkokin cinikayya ba. A saboda haka shugabanin suka yi alkawarin yin dukkanin bakin kokari domin farfado da shawarwarin. Bugu da kari sun kuma yi tur da Allah wadai da shirin nukiliyar Koriya ta arewa, to sai dai baá sanya shi a cikin daftarin yarjejeniyar da taron ya cimma ba, an gabatar da sukar lamirin ne kawar da fatar baka.