Kasashen Amurka da Sin sun soki rahoton Human Rights Watch | Labarai | DW | 19.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen Amurka da Sin sun soki rahoton Human Rights Watch

Fadar white House ta Amurka tayi Allah wadai da rahoton shekara ta 2005, na hukumar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch.

Fadar ta White House tace yin amfani da kalmomi na gallazawa da azabtarwa ga kasar ta Amurka, ba wani abu bane illa siyasa ce kawai.

Daukar wannan matakin dai daga bangaren mahukuntan na Amurka ya biyo bayan sukar da rahoton hukumar ta Human rights Watch yayi musu ne na take hakkokin bil adama, ta hanyar gallazawa fursunoni da kuma azzabtar dasu.

Bugu da kari rahoton na hukumar kare hakkin bil adaman ta kasa da kasa, ya kuma yi kakkausar suka ga kasar ta Amurka game da yadda take amfani da sunan yaki da aiyukan ta´adda amma tana take hakkokin bil adama.

Har ila yau rahoton mai shafi 500, ya ,kuma soki lamirin kasar Sin bisa irin yadda take take hakkokin bil adama a kasar. Game da hakan kuwa tuni mahukuntan na Sin suma suka yi Allah wadai da wannan suka.