1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Afurka a MDD

September 13, 2005

Murna ka iya komawa ciki dangane da bukatar kasashen Afurka na samun kujera ta dindindin a kwamitin sulhu idan har ba a cimma daidaituwa akan manufofin garambawul ga majalisar ba

https://p.dw.com/p/BvZf

Manufofi na garambawul ga tsare-tsaren MDD da sakatare-janar Kofi Annan ke fatan ganin an mayar da hankali kansu a zauren taron kolin shuagabannin kasashen majalisar a birnin New York yau, wanda za a fara yau laraba na fuskantar barazana sakamakon son zuciya a tsakanin kasashen. Shi kansa sakatare-janar Kofi Annan ya bayyana fatan samun wani kwakkwaran sakamako nan da karshen shekara, amma ya bayyana cewar muddin ba a cimma daidaituwa akan manufofin garambawul ga tsare-tsaren MDD a wannan shekarar ba, to zai dauki wasu shekaru da dama nan gaba, ana zaman tsammanin warabbuka.

Bayan kai ruwa rana da aka sha yi, kasashen Afurka sun cimma daidaituwa a taron kolinsu a birnin Addis Ababa a farkon watan agustan da ya wuce akan neman kujeru na dindindin guda biyu a kwamitin sulhu na MDD tare da wata cikakkiyar dama ta hawa kujerar naki akan duk wani kuduri na majalisar da bai gamsar da su ba. A baya ga haka kasashen na Afurka suna bukatar wakilcin kasashe biyu a tsakanin wakilai biyar da ba na dindindin ba a kwamitin na sulhu. Bukatar ta kasashen Afurka tayi daura da ta kasashe hudu da suka hada da Jamus da Japan da Brazil da kuma Indiya, wadanda ke sha’awar ganin an kara yawan membobin kwamitin sulhun zuwa kasashe 25 tare da sabbin wakilai na dindindin guda shida, wadanda ba za a ba su damar hawa kujerar naki ba. Akwai dai rarrabuwar ra’ayi tsakanin kasashen na Afurka akan wannan batu, inda a lokacin taron na Addis Ababa shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya ya ce wajibi ne kasashen su tattauna da sauran kasashen dake sha’awar samun kujera ta dindindin a kwamitin sulhu muddin suna fatan ganin an kai ga wani kwakkwaran sakamako mai gamsarwa. Amma kasar Aljeriya ta ce wajibi ne kasashen Afurka su dage akan bukatarsu ta farko, saboda bukatar tasu bata da wata dangantaka da ta sauran kasashe hudun da muka ambata can baya. To sai dai kuma manazarta na ganin wannan banbancin ra’ayi tsakanin kasashen Afurka na nuni ne cewar kasashen ba su da wani matsayi na bai daya tsakaninsu, kuma dagewarsu akan damar hawa kujerar naki ka iya zama karantsaye ga bukatar tasu. A baya ga kasashen Nijeriya da Masar da Afurka ta Kudu dake da angizo a yankunansu, akwai kuma kasashe kamar Kenya da Libiya da Angola da Senegal dake neman kujera ta dindindin a kwamitin sulhu na MDD. Wasu daga cikin kasashen dai sun bayyana cewar ko da ba a cimma biyan bukata ba, akalla nahiyar Afurka ta fito fili ta bayyana wa duniya bukatunta.