1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen Afrika ta tsakiya za su gana akan rikicin Tchadi da sudan

Chad/Sudan

Shugabannin kungiyar kasashen Afrika ta tsakiya data kunshi ´kasashe shida zasu yi wata ganawa ranar laraba mai zuwa a Chadi domin tattauna akan zaman dar dar din dake kara kamari tsakanin Chadi da Sudan.

Shugaban Chadi Idris Deby ne ya bukaci a gudanar da taron na musamman bayan wata ganawa da yayi da takwaransa na Kasar jamhuriyyar Afrika ta tsakiya Francois Bozize.

Mataimakin ministan harkokin kasashen waje na Chadi Ucienne Dillah ya shaidawa manema labarai cewa saboda wannan ganawar da shugabannin zasuyi Chadi ba zata sami damar halartar karamin taron kolin da kungiyar gamayyar Afrika za tayi a Libya ba game da yankin Darfur na sudan, dake iyakar Chadin , wanda ke fama da rikici tun shekara ta dubu biyu da uku.