kasashen Afrika na ci gaba da kokarin magance rikicin Darfur | Labarai | DW | 21.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

kasashen Afrika na ci gaba da kokarin magance rikicin Darfur

Shugabannin kasashen Sudan da Masar da Chadi da Libya da Eritrea sun hallara a birnin Tripoli a kokarinsu na samarda zaman lafiya a Darfur tare da sasanta tsakanin Chadi da Sudan.

Taron dai zai duba hanyoyin samun yarjejeniya tsakanin gwamnati da kungiyar NRF.

Kungiyar ta NRF gamaiyace ta kungiyoyin yan tawaye da suka ki amincewa da yarjejeniyar watan mayu,amma a halin yanzu ta amince ta tattauna da Khartoum amma bisa wata sabuwar yarjejeniya.

rikicin na Darfur ya koma matsalar yan gudun hijira da tawaye da yan fashi dake bazuwa kann iyakokin sudan da Chadi da kuma Jamhuriyar tsakiyar Afrika.

Yanzu haka dai MDD da AU suna ci gaba da matsawa Sudan lamba data amince da aikewa da dakarun MDD zuwa Darfur don kwantar da tashe tashen hankula na shekaru 3 da ya kashe dubban jamaa.