1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Kasashe na tir da sabon rikicin Isra'ila da Hamas

October 9, 2023

Shugabannin kasashen duniya sun yi kiran da a dawo kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, suna mai Allah wadai da hare-haren ba-zata da Hamas ta kaddamar a kan Isra'ila.

https://p.dw.com/p/4XHRn
Yankin zirin Gaza
Yankin zirin GazaHoto: Mahmud Hams/AFP/Getty Images

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya ce "ta'addanci ba zai taba zama hujja ba", yayin da sakataren harkokin tsaron Amurkar, Lloyd Austin ya ce kasar za ta "tabbatar da bai wa Isra'ila taimakon da take bukata don ganin ta kare rayukan fararen hularta."

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce kasarsa ta yi tir da hare-haren na Hamas, tare da nuna goyon baya ga Isra'ila.

Daga nashi bangare, shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, wanda jam'iyyarsa ta Fatah ke mulki a gabar yamma da kogin Jordan, ya ce Falasinawa na da 'yancin kare kansu daga abin da ya kira mamaya ta ta'addanci da dakarun Isra'ila ke yi musu.

Kasar China ta yi kiran bangaren Hamas da Isra'ila da su dakatar da kai wa juna farmaki, kamar yadda shi ma shugaban kungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki mahamat ya yi kiran da a koma teburin tattaunawa.

Akalla dai Isra'ilawa 700 ne suka salwanta kawo yanzu, yayin da bangaren Falasdinawa ke fadin ya rasa kimanin mutane 300.