Kasashe na gudanar da bukukuwan ranar ma’aikata ta Duniya | Labarai | DW | 01.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashe na gudanar da bukukuwan ranar ma’aikata ta Duniya

A daidai lokacin da ma'aikata ke gudanar da bukukuwan tunawa da ranar ma'aikata ta duniya,jami'an tsaro a wasu kasashe sun yi arangama da dandazon ma'aikatan da ke kokarin nuna fushin su kan halin da suke ciki.

A kasar Turkiya jami'an 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sanya kwalla gami da tankar ruwan zabi ga masu zanga- zangar tunawa da ranar ma'aikata ta duniya a yau,a yayin da a Faransa 'yan sanda ke cikin shirin ko ta kwana sakamakon masu zanga- zangar da ke son kara kawo sauyi na 'yancin ma'aikata.

Kama dai daga biranen Mosko zuwa Marseille da kasar Austriya gami da kasashen Afirka kungiyoyin ma'aikata sun gudanar da machi da ban daban domin tunawa da ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin waiwaye kan 'yancin ma'aikata a duk fadin duniya.

Kazalika a Koriya ta Kudu cen ma masu zanga- zanga ne suka nemi da gwamnati ta duba bukatun ma'aikatan kasar a yayin da suke tunawa da ranar ma'aikatan ta duniya.

An dai fara tunawa da ranar ma'aikatan ne a birnin Chicago na Amirka a shekara ta 1886 daga wata kungiya da ke bukatar yin aikin awa 8 a duk rana wanda yanzu haka kuma ta zamo ranar da ake tuwa da ita a duk fadin duniya.