Kasashe matalauta na jiran tsammani a dangane da alkawarin yafe musu bashi da manyan kasashe masu arziki suka yi | Siyasa | DW | 21.09.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kasashe matalauta na jiran tsammani a dangane da alkawarin yafe musu bashi da manyan kasashe masu arziki suka yi

A cikin wannan makon Ministoci kudi na duniya tare da Bankin duniya da asusun bada lamuni IMF zasu yi taro domin yanke hukunci akan makomar yafe bashi ga kasashe matalauta.

Paul Wolfowitz Shugaban Bankin Duniya

Paul Wolfowitz Shugaban Bankin Duniya

Tun kimanin shekaru 60 da suka shude, taron Ministocin kudin na duniya ya kasance babban alámari ga gwamnatoci da alúmomi na duniya ba don komai ba sai don manufofin wadannan hukumomi na yin tasiri sosai ga tattalin arzikin kasashen na duniya. Taron na bana, wanda zai gudana daga ranar 24-25 ga wannan watan yana da matukar muhimmaci sosai, dalili kuwa shi ne, a watan Yulin da ya gabata, kungiyar G8 ta kasashe masu cigaban masanaántu na duniya suka amince su yafe bashi ga kasashe 18 mafi talauci a duniya wadanda bankin duniyar da asusun bada lamuni IMF da kuma bankin raya kasa na Afrika suke bin su bashi. Taron zai yi muhawara akan shawarar ta kungiyar G8, inda Ministocin zasu yi nazari akan yiwuwa ko rashin yiwuwar aiwatar da kudirin na G8. Akwai dai shakku da ake baiyanawa kama daga cikin hukumomin kudaden har ya zuwa kungiyoyi masu zaman kan su a game da makomar yafe bashin .

Wani rahoton bankin duniyar da aka tseguntawa yan jarida a makon da ya gabata, ya nuna cewa idan aka yafewa kasashen bashin da ake bin su wanda ya tasamma dala biliyan 40, to kuwa zai raunana jarin kungiyar taimakon raya kasa IDA wanda wani reshe ne na bankin duniyar wanda a kowace shekara ya kan bada bashi mai sassauci ga kasashe matalauta, dama dai kasashe kamar su Belgium da Norway da Switzerland da kuma Netherland suka soki lamirin yafe bashin dari bisa dari ba kuma tare da wata hujja ba. Hakazalika sun bukaci sanya dokoki masu tsauri da zaá yi laákari da su wajen yafe bashi ga kasashe a nan gaba.

Babban siratsin da a yanzu yake gaba na aiwatar da yafe bashin shi ne cewa, a yayin da daukacin kasashen kungiyar G8 suke da kaso 50 cikin 100 na kuriá a hukumomin biyu na bankin duniya da kuma asusun bada lamuni IMF, yanke shawara ko zartar hukunci kai tsaye akan batun yafe bashi, na bukatar amincewar rinjayen kaso 85 cikin dari na kuriún wakilan hukumomin. Har ila yau, yayin da a hannu guda kasashen turai suke da mafi rinjayen kuriú, a daya hannun kuma, kasashen da basa cikin kungiyar G8 ka iya zama Kandagarki wajen cimma nasarar aiwatar da yarjejeniyar.

Kasashe dake cikin kungiyar ta G8 sun kunshi Britaniya da Rasha da Faransa da Jamus sauran su ne Amurka da Japan da Italiya da kuma Kanada. Idan har wannan batu na yafe bashi bai samu nasara ba, to kuwa zai kasance babban abin takaici, ba kawai ga kasashe 18 da aka yiwa alkawarin yafe musu bashi ba, har ma da sauran kasashe matalauta na duniya, wadanda yawancin alúmomin su suke rayuwa akan kasa da Dala daya a rana, wanda ke nufin cewa zasu cigaba da kasancewa cikin kangin talauci, bugu da kari, zai jawowa kungiyar ta G8 mummunan bakin jini na gazawa wajen cika alkawuran da tayi.

A waje guda dai kungiyoyin alúma masu zaman kan su na baiyana cewa matakan biyan bashi ta hannun hukumomin kudade na Bankin duniya da asusun bada lamuni IMF, na yiwa kasashe tarnaki wajen samun nasarar shirin raya kasa na Millenium goal. Daga cikin kasashe 18 da aka tantance domin yafe musu bashi, guda goma sha hudu kasashe ne na Afrika yayin da ragowar kasashen hudu suke yankin latin Amurka da kuma Carribean. A matsayin da ake ciki, dukkanin kasashen 18 sun cika sharudan da ake bukata daga gare su wadanda suka hada da sayar da kadarorin gwamnati. A cewar wata kungiya mai zaman kan ta ta Britaniya wadda kuma ke fafutukar yaki da talauci, tace a kalla akwai kasashe guda 62 wadanda ke bukatar a yafe musu bashi idan har ana bukatar su cimma kudirin raya kasa na Millenium nan da shekara ta 2015.