Kasashe masu tasowa sun hau kujerar na ki a Majalisar Dinkin Duniya | Labarai | DW | 29.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashe masu tasowa sun hau kujerar na ki a Majalisar Dinkin Duniya

Kasashe masu tasowa a MDD sun yi fatali da shawarwarin yin garmabawul a MDD don bawa babban sakatarenta Kofi Annan karin ikon sa ido akan kasafin kudin majalisar. Wannan mataki da suka dauka bayan an shafe kwanaki ana tabka muhawwara akan wanann batu, zai kara tsananta bambamcin ra´ayi tsakanin kasashe masu arziki da matalauta a cikin gamaiyar ta kasa da kasa. Da farko kasashe masu arziki sun yi gargadin cewa kin amincewa da wannan shawara ka iya jefa MDD cikin wani mummunan hali na rashin kudi.